Kamfanin Dillancin Labaran ƙasa da ƙasa na Ahlul-Baiti (AS) – ABNA - ya habarta cewa: Sayyid Abbas Araghchi a shafinsa na sada zumunta ya rubuta: Yarjejeniyar Islamabad ba ta taɓa kusantar kammaluwa kamar yadda take a yanzu ba. Har zuwa a kammala ta, dole ne kafafen yada labarai su guji shiga cikin hasashe game da abubuwan da ke cikinta.
Yayi ishara da cewa: A cikin tsarinmu na alhakin da ke kanmu da gaskiya, dukkan cikakkun bayanai za a bayyana su ga jama'a a lokacin da ya dace.
Trump shi ma ya mayar da martani ga wannan sako ta hanyar sake bugawa a shafinsa.
Shi ma Firayim Ministan Pakistan Shehbaz Sharif ya bayyana cewa: Za mu iya tabbatar da cewa an cimma rubutun ƙarshe da aka amince da shi; muna sane da kanfen din yada bayanan karya.
Shehbaz Sharif firayim ministan Pakistan ya ce: A daidai lokacin da Pakistan ke gudanar da ƙoƙarce-ƙoƙarce na sasanci, muna da cikakken masaniya game da yunkurin yada bayanan karya da jita-jita daga waɗanda suke son lalata yarjejeniyar zaman lafiya. Idan muka yi watsi da waɗannan surutai, za mu iya tabbatar da cewa an cimma rubutun ƙarshe da aka amince da shi na yarjejeniyar zaman lafiya.
Pakistan yanzu tana aiki tare da bangarorin biyu don kammala matakai na gaba. Sulhun bai taɓa kusantar haka ba kamar yadda yake a yanzu.
.....................
Your Comment